Connect with us

Labarai

Kwankwaso ya buƙaci kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC ya mayar da hankali wajen kare Atiku kan zarge-zargen da ake masa

Published

on

Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya buƙaci kwamitin yaƙin neman zaɓen dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC ya mayar da hankali wajen kare ɗan takararsu, Atiku Abubakar, kan zarge-zargen da ake yi masa, maimakon sukar sa da ɗan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a martanin da ya mayar kan zargin da ADC ta yi masa na ƙoƙarin raba kan ‘yan adawa domin taimaka wa Shugaba Bola Tinubu samun nasarar zaɓe a shekarar 2027.

 

Tsohon gwamnan na Kano ya ce jam’iyyarsa ba za ta janye takararta ga ADC ko wata jam’iyya ba, yana mai cewa gwamnatin APC ta gaza wajen tafiyar da Najeriya, yayin da ADC ba ta da wani tsari mai kyau ga ‘yan ƙasar.

 

Ya kuma ce tikitin Obi da Kwankwaso na da ƙarfin lashe zaɓen 2027, tare da alƙawarin magance matsalolin tsaro, ilimi, noma, kiwon lafiya da tattalin arziki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!