Connect with us

Labarai

APC za ta bai wa Shugaba Tinubu takardar shaidar nasara a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa

Published

on

Jam’iyyar APC za ta bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu takardar shaidar nasara da kuma tutar jam’iyyar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen shekarar 2027 a yau Lahadi.

Ta cikin wata sanarwa da Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ne ya fitar, ta ce kwamitin gudanar da zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa ne zai gabatar da takardar da tutar a wajen wani taro da za a gudanar a Cibiyar Taro ta Bola Ahmed Tinubu International Conference Centre da ke Abuja, bayan kammala tattara sakamakon zaɓen fidda gwani daga faɗin ƙasar nan.

Ana sa ran gwamnoni na jam’iyyar APC, mambobin Kwamitin Zartarwa na Ƙasa, Kwamitin Ayyuka na Ƙasa, mambobin Majalisar Dokoki ta Ƙasa da sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar za su halarci taron.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!