Connect with us

Labarai

NDLEA ta kama dillalan miyagun kwayoyi 38 a Kano

Published

on

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen Kano ta ce ta kama mutane 38 a wani samame na kwanaki biyu da ta gudanar a wasu wuraren da ake zargin hada-hadar miyagun kwayoyi a cikin birnin Kano, gabanin bukukuwan Eid al-Kabir. Samamen ya gudana karkashin shirin “Operation Sharar Mafaka” ƙarƙashin jagorancin kwamandan rundunar, CN DY Lawal.

Sanarwar da jami’in hulda da jama’a na hukumar a Kano, Sadiq Muhammad Maigatari ya fitar, ta ce an kai samamen ne a yankunan Fagge, Filin Idi, Gyadi Gyadi, Hotoro, Tashar Rami, Audu Bako Secretariat, Hauren Gadagi, Kofar Mata, Sheka da kuma Farm Center. Hukumar ta ce ta kwato wasu miyagun kwayoyi da makamai na gargajiya da suka hada da cannabis sativa, Exol-5, Diazepam, “Suck and Die”, roba mai wari da kuma wasu makamai da aka kera a gida.

Kwamandan rundunar, CN DY Lawal, ya ce sun tsaurara samamen ne domin hana bata-gari amfani da shagulgulan Sallah wajen aikata laifuka da yada miyagun kwayoyi. Ya kara da cewa hukumar za ta ci gaba da kai samame domin tabbatar da zaman lafiya yayin bukukuwan Sallah, yayin da bincike ke ci gaba da gudana kan wadanda aka kama domin gurfanar da su a kotu idan bukatar hakan ta taso.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!