Labarai
Rundunar Sojin Najeriya sun fatattaki Yan-ta’adda a Zamfara

Dakarun sojoji da ke gudanar da aikin kawar da ‘yan bindiga daga garin Bukuyum a jihar Zamfara sun yi artabu da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne da ke ƙoƙarin tserewa a yankin dajin Tsilligidi.
Rahotanni sun ce bayan sojojin sun samu bayanan sirri kan motsin ‘yan bindigar, suka nufi maboyarsu.
Sojojin sun tare su tare da yin musayar wuta mai tsanani. A yayin artabun, an kashe da dama daga cikin ‘yan bindigar, yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.
An bayyana cewa wannan farmaki wani ɓangare ne na ƙoƙarin da sojoji ke yi na rusa sansanonin ‘yan bindiga da kuma dawo da zaman lafiya a al’ummomin da ke fama da matsalar tsaro a jihar Zamfara. Har yanzu dai ana ci gaba da bibiya da share dazukan domin kamo waɗanda suka tsere.
You must be logged in to post a comment Login