Labaran Wasanni
Arsenal ta hana Liverpool hada maki 100 a firimiyya
Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dake kasar Ingila ta kawo wa kungiyar kwallon kafa ta Liverpool cikas wajen kokarin da take na hada maki 100 a gasar Firimiya ta kasar Ingila.
Arsenal dai ta chasa Liverpool da ci 2-1 a ci gaba da gasar ta Firimiya mako na 36 a daren Laraba.
Tuni dai Liverpool ta lashe gasar Firimiyar Ingila ta bana bayan da ta kwashe shekaru 30 ba tare da ta dauki gasar ba.
Dan wasan Liverpool Sadio Mane ne ya fara zura kwallo a wasan zagayen farko cikin minti na 30, kafin daga bisani dan wasan Arsenal, Lacazette ya farke a minti na 32, inda dan wasa Nelson ya kara wa Arsenal kwallo ta biyu a minti na 44 daf da za a tafi hutun rabin lokaci.
Zuwa yanzu dai wasa 2 ne ya rage a karkare gasar Firimiya, inda Liverpool take jagaba a gasar da maki 93 cikin wasanni 36 da ta buga.
Ita kuwa Arsenal ta na mataki na 9 da maki 53 wanda kuma take fatan kara matsawa gaba a gasar, domin karewa a mataki na 6 ko 5, domin ganin ta halarci gasar cin kofin Europa a kakar wasanni mai zuwa.
Jim kadan bayan tashi daga wasan, mai horas da Liverpool, Jurgen Klopp ya nuna rashin jin dadin sa bisa rashin nasarar da kungiyar ta yi, sai dai ya jinjinawa ‘yan wasan sa bisa kokarin da suka nuna a wasan.
You must be logged in to post a comment Login