Labaran Kano
Asibitin Aminu Kano ya raba maganin ciwon kunne kyauta
Shugaban shashin ciwon kunne na asibitin Malam Aminu Kano Dakta Abdulhakim Aluko ya ja hankalin iyayen yara da malam makaranta da su rika kula da lafiyar kunnen yaransu.
Ya ce mutane da yawa suna fama da matsalar ciwon kunne amma basa son zuwa asibiti a duba lafiyarsu wanda haka ke zama babbar barazana ga lafiyar kunne.
Dakta Abdulhakim Aluko ya bayyana haka ne lokacin bikin ranar Ji ta duniya wanda ya gudana a garin Gurin Gawa dake karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano.
Ya kara da cewa sun shirya wannan taro ne domin tunawa da ranar ji ta duniya da kuma yin kwajin ciwon kunne kyauta tare da bayar da magani ga al’ummar garin na Gurin Gawa.
A nasa jawabin Shugaban karamar hukumar Kunbotso Alhaji Kabiru Ado ya nuna farin cikinsa kan yadda aka zabi karamar hukumarsa domin yin wannan taro tare da bayar da tallafin.
Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa yara da tsofaffi da dama ne su kaci gajiyar samu wannan magani kyauta
You must be logged in to post a comment Login