Labarai
ASUU ta zargi gwamnatin tarayya da ƙin cika alkawura

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasar nan reshen jihar Sokoto, wato ASUU Zone 10, ta zargi gwamnatin tarayya da gaza cika alkawuran da aka cimma tsakanin bangarorin biyu musamman kin kaddamar da kwamitin sa ido da aiwatar da yarjejeniyoyi.
Shugaban shiyyar, Farfesa Abubakar Sabo, ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a Sokoto, inda ya nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da yin watsi da bukatun jin dadin malaman jami’o’i. Ya ce har yanzu ba a mayar da wasu alawus-alawus kamar CATA da EAA da kuma alawus din farfesoshi cikin tsarin albashin wata-wata ba.
Kungiyar ta bayyana cewa tun daga shekarar 2009 take fafutukar neman biyan bukatunta, amma har yanzu gwamnati ta gaza wajen warware matsalolin
Kungiyar ta kuma bukaci a biya bashin karin albashi na kaso 25 zuwa 35 cikin 100, da kudaden karin girma, da gibin albashi da matsalolin da suka samo asali daga tsarin IPPIS da kuma cire-ciren kudade daga albashi.
ASUU ta kuma nuna rashin amincewa da wasu manufofin ilimi da gwamnatin ke kokarin aiwatarwa, ciki har da soke amfani da harshen uwa wajen koyarwa.
You must be logged in to post a comment Login