Connect with us

Labarai

Shugaba Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar JAMB

Published

on

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada Farfesa Segun Aina a matsayin sabon shugaban hukumar shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta JAMB.

Wannan na cikin wata  sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Mista Bayo Onanuga ya fitar yau  Alhamis.

Ta cikin sanarwar mista Bayo ya ce,  Farfesa Aina kwararre ne a fannin ilimin kwamfuta da fasahar gudanar da jarabawa, tare da gogewa a bangaren sauye-sauyen cibiyoyi da inganta ayyukan gwamnati ta hanyar amfani da fasaha.

Sanarwar ta kuma ce,  Aina, wanda zai cika shekaru 40 a watan Yuli, ya kuma karanci ilimin Kwamfuta a Jami’ar Kent da ke Birtaniya, sannan ya samu digirin na biyu a Jami’ar Loughborough a bangarorin Internet Computing, Haka kuma ya halarci shirin horas da shugabanci a Lagos Business School.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!