Labarai
Jihar Kaduna ta kammala jigilar Alhazan ta daga Madina zuwa Makkah

Hukumar jin dadin Alhazan jihar Kaduna ta bayyana cewa ta kammala jigilar dukkanin Alhazan jihar daga Madina zuwa Makkah a jiya Juma’a domin ci gaba da gudanar da aikin Hajjin bana.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Kaduna, Ibraheem Musa, ya fitar, an ce an samu nasarar jigilar Alhazan cikin sauki ne sakamakon shiri tun da wuri da kuma goyon bayan gwamnatin jihar ga aikin Hajjin 2026.
Daraktan ayyuka na hukumar Alhazai ta jihar Kaduna, Abubakar Yusuf, ya ce Alhazan sun kwashe kwanaki hudu na wajibi a Madina kafin a fara jigilar su zuwa Makkah rukuni-rukuni, inda rukuni na karshe zai tashi a yau Juma’a.
Ya kara da cewa tun kafin fara aikin Hajji aka rika gudanar da shirye-shiryen wayar da kan maniyyata a fadin jihar, domin ilmantar da su kan dokokin Saudiyya da yadda za su gudanar da kansu yayin ibadar Hajji.
Hukumar ta kuma bayyana cewa tawagar Hajjin jihar Kaduna tare da jami’an hukumar sun ziyarci wani Alhaji mai suna Sani Garba wanda aka kwantar a asibitin Almiqati da ke Madina, inda daga bisani aka sallame shi sannan aka wuce da shi zuwa Makkah ranar Alhamis.
An kuma bayyana cewa an sauke Alhazan Kaduna ne a unguwar Misfalah da ke Makkah, kusa da titin Ibrahim Khalil, wanda ke da nisan tafiya kadan zuwa Masallacin Harami.
You must be logged in to post a comment Login