Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kogi ta fara binciken mutuwar iyalan da suka mutu bayan cin abinci

Published

on

Gwamnatin Jihar Kogi ta bayar da umarnin gudanar da bincike kan mutuwar mutane huɗu daga gida ɗaya a yankin Ihima, da ke ƙaramar hukumar Okehi.

Rahotanni sun ce mutanen sun rasu ne bayan cin abincin amala, yayin da karen iyalin ya mutu bayan cin abincin da ake zargin shi ma ya ci.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Sadarwa na jihar, Kingsley Fanwo, ya ce Gwamna Ahmed Ododo ya umarci Kwamishinan Lafiya da ya fara cikakken bincike.

Ya ce binciken zai duba yiwuwar mutuwar ta samo asali ne daga gubar abinci ko kuma gurɓacewar abincin da iyalin suka ci.

Kwamishinan ya ce za a binciki samfuran abincin da sauran hujjojin da ake da su, domin gano ainihin musabbabin mutuwar.

Gwamnatin ta kuma yi kira ga jama’a da su kwantar da hankula, tare da guje wa yin hasashe kan lamarin har sai an kammala binciken.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!