Labarai
Tinubu ya soki kalaman Atiku na bude iyakokin kasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta yi watsi da alkawarin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, na sake buɗe iyakokin Najeriya idan ya lashe zaɓen 2027.
Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan yaɗa labarai, Sunday Dare, ya ce gwamnatin tarayya ta sake buɗe mafi yawan iyakokin ƙasar tun ranar 14 ga Maris na 2024, kuma ba ta sake rufe su ba.
Martanin ya biyo bayan furucin Atiku na cewa zai sake buɗe iyakokin domin farfaɗo da kasuwancin ƙetare da tallafa wa ‘yan kasuwa. Ya kuma yi alkawarin bunƙasa tashoshin jiragen ruwa da ke kudancin Najeriya domin daidaita shigo da kayayyaki da safarar su.
Sunday Dare ya ƙalubalanci Atiku da ya bayyana matakan da zai ɗauka wajen inganta tsaron iyakoki, tare da yaɗa bayanan sirri da haɗin gwiwar jami’an tsaro.
You must be logged in to post a comment Login