Labarai
Atiku ya ƙalubalanci gwamntin shugaba Tinubu kan tallafin Fetur

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ƙalubalanci gwamnatin tarayya da ta bayyana wa ’yan Najeriya yadda aka kashe kuɗaɗen da aka samu daga cire tallafin man fetur.
A cikin wata sanarwa da babban mataimakinsa kan harkokin sadarwa, Phrank Shaibu, ya fitar a madadinsa, Atiku ya ce gwamnati ta cire tallafin tare da neman ’yan Najeriya su jure wahalhalun da hakan ya haifar, bisa alkawarin cewa za a yi amfani da kuɗin wajen ayyukan ci gaba.
Atiku ya ce tashin farashin man fetur, sufuri da abinci ya ƙara jefa ’yan Najeriya cikin wahala, yana mai tambayar gwamnati inda kuɗin jama’a suke.
Ya kuma ƙalubalanci gwamnatin Tinubu da ta bincike shi idan tana da hujjar aikata ba daidai ba, maimakon ta riƙa maimaita zarge-zargen da suka shafi lokacin da yake mataimakin shugaban ƙasa.
You must be logged in to post a comment Login