Connect with us

Labarai

Atiku ya kalubalanci matsayar gwamnonin PDP

Published

on

Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya kalubalanci  matsayar  gwamnonin jam’iyyar PDP wadanda suka nesanta jam’iyyar daga kawancen da Atikun ke yi. 

A ranar Litinin ne kungiyar gwamnonin jam’iyyar ta PDP karkashin jagorancin gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed, suka bayyana cewa jam’iyyar ba za ta shiga cikin wata hadaka da kowace jam’iyya ba.

Sai dai a martanin da ya mayar, Atiku Abubakar ta hannun mataimakinsa kan yaɗa labarai Paul Ibe, ya jaddada bukatar fadada tattaunawar  domin samun matsaya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!