Connect with us

Labarai

Atiku ya soki ƙarin kuɗin WAEC da NECO zuwa N50,000

Published

on

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, , ya yi Allah-wadai da rahotannin da ke cewa gwamnatin tarayya na shirin sanya kuɗin rajistar jarabawar WAEC da NECO ya zama Naira 50,000 ga kowane ɗalibi daga shekarar 2027. Ya ce hakan zai ƙara wahalar da iyalai tare da hana miliyoyin yara samun ilimi.

Atiku ya bayyana cewa ƙarin kuɗin jarabawa da kuma ƙarin kuɗin makarantun Unity Colleges ba su dace da halin matsin tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke ciki ba. A cewarsa, ilimi shi ne babban makamin yaƙi da talauci, kuma gwamnati ta kamata ta rage shingen da ke hana yara zuwa makaranta maimakon ƙara musu nauyi.

Ya kuma yi kira ga Shugaba da ya janye shirin ƙarin kuɗin WAEC da NECO tare da sake duba kuɗin makarantun Unity Colleges. Atiku ya buƙaci gwamnati ta ƙara zuba jari a fannin ilimi, ta faɗaɗa cibiyoyin karatu, ta ɗauki ƙarin malamai, tare da tabbatar da cewa babu wani yaro da za a hana samun ilimi saboda ƙarancin kuɗi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!