Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da yin ƙarin kuɗin rajistar WAEC da NECO

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ƙara kuɗin rajistar jarabawar WAEC da NECO ta shekarar 2027, domin ba da damar gudanar da ƙarin tattaunawa da masu ruwa da tsaki kafin ɗaukar matsaya ta ƙarshe.

Ma’aikatar Ilimi ta kasa ce ta bayyana cewa ta janye wasiƙar da ta fitar a ranar 18 ga watan Yunin 2026 kan ƙarin kuɗin rajistar, bayan korafe-korafe da ra’ayoyin da jama’a suka bayyana game da shirin.

Ma’aikatar ta ce an gabatar da shawarar ne saboda hauhawar kuɗaɗen gudanar da jarabawar ƙasa, ciki har da sufuri, tsaro, buga takardun jarabawa, amfani da fasaha da kuma tabbatar da ingancin jarabawar.

Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya umarci a dakatar da shirin domin bai wa dukkan masu ruwa da tsaki damar ba da gudunmawarsu kan kudirin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!