Labarai
Peter Obi ya buƙaci Shugaba Tinubu ya ya yi bayani kan tarihin karatunsa

Ɗan takarar shugabancin kasar nan a jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya fito fili ya yi bayani kan batutuwan da suka shafi tarihin karatunsa, musamman takardun da suka shafi makarantar firamare da sakandare.
Peter Obi ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a ranar Laraba.
Dan takarar bangaren adawar ya ce yunƙurin hana jama’a samun wasu bayanan kotunan ƙasashen waje da suka shafi tarihin shugaban abin kunya ne ga kasar nan da Kuma siyasar ta.
You must be logged in to post a comment Login