Labarai
Atiku ya zargi Shugaba Tinubu da kauce wa fuskantar yan Najeriya wajen yin bayanin halin matsin tattalin arziki

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya zargi Shugaba Bola Tinubu da kauce wa fuskantar ’yan Najeriya kai tsaye domin ya yi musu bayanin halin matsin tattalin arzikin da suke ciki, duk da cewa yana neman sake zaɓensa a wa’adin mulki na biyu a shekarar 2027.
Atiku ya ce bai kamata shugaban ƙasar ya nemi ƙarin wa’adin mulki na shekaru huɗu ba tare da ya yi wa ’yan Najeriya bayanin irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu cikin shekaru uku da rabi da ta shafe tana mulki ba.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma soki yadda ake ci gaba da fuskantar tsadar rayuwa, yana mai cewa ’yan Najeriya na da haƙƙin sanin abin da gwamnatin ta cim ma kafin su yanke shawarar sake ba ta damar mulki.
Sai dai kalaman na Atiku na zuwa ne yayin da jam’iyyun siyasa ke ci gaba da shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
You must be logged in to post a comment Login