Connect with us

Labarai

Gwamna Abba ya ƙaddamar da shirin bai wa ɗalibai shawarwarin zaɓen sana’o’i da kwasa-kwasai

Published

on

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da shirin bai wa ɗaliban makarantun sakandare shawarwarin zaɓen sana’o’i da kwasa-kwasai masu alfanu domin taimaka musu wajen shiryawa da kuma cin jarabawar shiga manyan makarantu ta UTME.

Gwamnan, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar, ya wakilta, ya ce shirin zai ƙarfafa tsarin ba da shawarwari a makarantu, tare da horar da masu ba ɗalibai shawara domin taimaka musu zaɓen fannonin karatu da sana’o’in da suka dace da su.

Abba Yusuf ya bayyana cewa ilimi bai tsaya ga samar da malamai da azuzuwa ba, yana mai cewa akwai buƙatar ɗalibai su fahimci baiwarsu da abubuwan da suke sha’awa kafin zaɓen kwas ko babbar makarantar da za su shiga.

Ya kuma buƙaci iyaye da malamai da masu ba da shawara su haɗa kai wajen jagorantar matasa, musamman wajen magance shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da sauran munanan ɗabi’u, tare da shirya su domin cin gajiyar sabbin damar sana’o’i da fasaha mai tasowa, ciki har da fasahar AI.

Gwamnan ya buƙaci ɗalibai su mayar da hankali wajen karatu, tare da neman shawarwarin ƙwararru maimakon bin ra’ayin abokai, yana mai kira ga masu ruwa da tsaki a harkar ilimi da su tabbatar da amfanin shirin ya isa ga ɗalibai a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!