Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarayya ta sake musanta shirin kara kudin lantarki

Published

on

Gwamnatin tarayya ta sake tabbatar da cewa ba ta da shirin ƙara kuɗin wutar lantarki a faɗin Najeriya, ta na mai cewa abin da ta fi mayar da hankali a kai shi ne inganta samar da wutar lantarki maimakon ƙara wa ’yan Najeriya kuɗaɗen da suke biya.

 

Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis, yayin bikin fara aikin samar da ƙananan tashoshin wutar lantarki guda biyar a birnin Ibadan, na jihar Oyo.

 

Ministan ya ce gwamnati na aiki domin tabbatar da samun wutar lantarki dare da rana, inda ya buƙaci ’yan Najeriya su yi watsi da rahotannin da ke cewa ana shirin ƙara kuɗin wutar lantarki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!