Labarai
Fiye da dakarun Amotekun 200 sun rasa rayukansu yayin yaki da matsalolin tsaro- Gwamna Makinde

Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa sama da jami’an rundunar tsaro ta Amotekun 200 ne suka rasa rayukansu yayin yaki da matsalolin tsaro a jihar.
Makinde ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyarar jaje ga iyalan dalibai da malamai da aka sace daga wasu makarantu uku a yankin Oriire na Ogbomoso.
Gwamnan ya yi kira ga dukkan matakan gwamnati da su hada kai domin ceto wadanda aka sace, yana mai cewa wannan ba lokaci ba ne na dora wa juna laifi. Ya kuma jaddada cewa an kafa rundunar Amotekun ne a shekarar 2020 a matsayin mafita ta wucin gadi bayan gazawar samar da ‘yan sandan jihohi.
Hakazalika, Makinde ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta aiwatar da tsarin ‘yan sandan jihohi domin karfafa yaki da matsalolin tsaro a fadin kasar.
You must be logged in to post a comment Login