Connect with us

Labarai

Sojoji sun ceto Mutane 22 daga hannun ’Yan Bindiga a Sokoto

Published

on

Dakarun sojin Najeriya na Operation FANSAN YAMMA sun ceto mutane 22 da ’yan bindiga suka sace a hare-hare daban-daban da suka faru a ƙananan hukumomin Sabon Birni da Isa na jihar Sokoto.

A cewar sanarwar da Jami’in Yaɗa Labaran Operation FANSAN YAMMA, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar a ranar Asabar 20 ga Yunin 2026, ’yan bindiga sun tare wasu motoci biyu a ƙauyen Kura Mota da ke kan hanyar Sabon Birni zuwa Shinkafi, inda suka yi awon gaba da wasu fasinjoji.

Sanarwar ta bayyana cewa mutum ɗaya ya rasa ransa a harin kafin dakarun soji su isa wurin tare da kaddamar da farmakin bibiyar maharan, da taimakon sa ido ta sama.

Sakamakon matsin lambar da sojojin suka yi wa maharan, sun yi watsi da fasinjoji 17 da suka sace tare da tserewa zuwa cikin daji.

Hakazalika, a ƙauyen Chohi da ke ƙaramar hukumar Isa, dakarun sun yi nasarar ceto manoma biyar da wasu ’yan bindiga suka yi ƙoƙarin sacewa yayin da suke gudanar da ayyukansu a gonaki.

Bayan nasarar ceton mutanen, sojojin sun ci gaba da sintiri a ƙauyukan Gidan Rana da Gidan Sale domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankunan.

Wannan nasara ta ƙara nuna ƙoƙarin jami’an tsaro wajen daƙile ayyukan ’yan bindiga da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a Arewa maso Yamma.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!