Addini
Azumi: A fara duban jinjirin watan Ramadan – Sarkin Musulmi
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya umarci al’ummar Musulmi da su fara duban jinjirin watan Ramadan na shekarar 1442AH daga Litinin din nan.
Alhaji Sa’ad Abubakar ya ba da wannan umarnin ne ta cikin wata sanarwa da Farfesa Sambo Junaidu, shugaban kwamitin shawara kan harkokin Addini a Majalisar Masarautar Sakkwato ya sanyawa hannu.
“Muna sanar da al’ummar Musulmi cewa Litinin, 12 ga Afrilu, wacce ta yi daidai da ranar 29 ga Sha’aban 1442AH za ta kasance ranar neman sabon wata na Ramadan a shekarar 1442AH saboda haka, ana bukatar Musulmai da su fara duban jinjirin wata a ranar Litinin kuma su kai rahoton ganin sa ga shugaban Gundumar su don isarwa ga Sarkin Musulmi” in ji sanarwar.
Ta cikin sanarwar, Farfesa Sambo Junaidu ya ba da lambobin wayar da za a iya amfani da su kai tsaye don kai rahoton ganin sabon watan ga kwamitin.
Lambobin sune 08037157100, 07067416900, 08066303077, 08036149757, 08035965322 da 08035945903.
You must be logged in to post a comment Login