Addini
AZUMI: Kana kara farashi za mu daina sayar maka da kaya – Abdussamad Rabi’u ga diloli.

Shugaban rukunin kamfanonin BUA Alhaji Abdussamad Isyaku Rab’iu ya yi barazanar kwace lasisin duk wani abokin hulda da kamfanin sa da ya kara farashin kayayyakin da kamfanin ke sayarwa a lokacin azumin watan Ramadan.
Alhaji Abdussamad Rabi’u ya kuma tabbatar da cewa kamfaninsa ya samar da isashshen kayayyaki ga abokan huldarsa wanda zai biya bukatun dukkan nin jama’ar kasar nan a lokacin azumi.
Alhaji Abdussamad Rabi’u wanda wakilin kamfanin na BUA mai kula da yankin arewacin kasar nan Alhaji Muhammad Adakawa ya yi magana a madadin sa, ya bayyana hakan ne a yau laraba lokacin da ya ke zantawa da jaridar solacebase a nan Kano.
Alhaji Abdussamad Rabi’u ya kuma ce kamfanin na BUA ya samar da kayayyaki masu yawa da suka hada da: Sikari, taliya, fulawa da sauransu .
‘‘Ina tabbatar muku cewa muna da kayayyaki masu yawa a ma’ajiyar mu da ke Sharada wadda zai biya bukatun al’ummomin jihohin Kano, Kebbi, Jigawa, Yobe, Borno, Zamfara, da kuma Katsina har ma da sauran jihohi da ke arewacin kasar nan’’ a cewar sa.
You must be logged in to post a comment Login