Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Covid-19: Gidauniyar BUA ta tallafawa Kano da kayayyaki na naira biliyan biyu

Published

on

Gidauniyar BUA karkashin jagorancin Alhaji Abdussamad Isyaka Rabiu ta ce a shirye take ta tallafawa Kano akan kariyar cutar Corona

Wakilin shugaban gidauniyar Dr. Aliyu Idi Hong ne ya bayyana hakan da yammacin Litinin dinnan lokacin da suka kawo kayan tallafin motocin daukar marasa lafiya biyar da motocin gudanar da aiki ashirin.

Dr. Hong ya ce a dunkule gidauniyar ta baiwa Kano tallafin naira biliyan biyu wanda a ciki ne aka sayi wannan kayayyakin.

A nasa bangaren gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce wannan rana ce mai muhimmanci ganin yadda ‘yan asalin Kano ke tallafawa jihar don yaki da cutar.

Wakiliyar mu Zahra’u ta rawaito cewa kamfanin fulawa na Golden Penny da makarantar horar da hafsoshin soji ta NDA sun kawowa jihar Kano kayayyakin kula da lafiya da gwaje-gwajen cutar Corona.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!