Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Baɗala: An cafke babban jami’in Hisbah da matar aure a Otel

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta cafke babban jami’in hukumar Hisbah ta jihar Kano mai kula da kamen almajirai da mata masu zaman kansu.

An cafke babban jami’in ne a wani Hotel da ke unguwar Sabon Gari tare da wata matar aure a nan Kano.

Babban Kwamandan hukumar Hisbah na jiha Malam Muhammad Haruna Ibn Sina ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni suka kafa kwamiti na mutum biyar domin yin bincike.

Ibn Sina ya bayyana takaicinsa kan faruwar lamarin, har ma ya ce, Kwamitin da aka kafa zai yi aiki cikin kwanaki uku sannan ya bada rahoton sa a kai, domin ɗaukar matakin da ya dace.

Rahotonni sun ce, mijin matar ne ya yi ƙorafi ga ƴan sanda, wanda su kuma suka bi sahu har suka cafke wanda ake zargin.

Karin labarai:

Mun karbi korafe-korafe fiye da kowanne lokaci daga farkon shekara nan – Hisbah

Kano: Hisbah ta yi sulhu da masu gidajen kallo da wuraren shaƙatawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!