Labarai
Dimokuraɗiyyar Najeriya, cigaban mai haƙan rijiya ne – Dr. Abbati Baƙo
Masanin kimiyyar siyasar nan a Kano Dakta Abbati Bako ya bayyana cewar ba’a samu wani ci gaba ba a tsawon shekaru 21 da aka yi ana gudanar da mulkin dimokuradiyya a kasar nan, idan a ka kwatanta da wasu kasashen duniya.
Dakta Abbati Bako ya bayyana hakan ne a ranar Talata, jim kadan bayan kammala Shirin ‘Barka da Hantsi’ na nan Freedom Radio, wanda ya tattauna al’amuran da suka shafi ci gaban siyasa.
Ya kara da cewar ta bangaren wayar da kan al’umma kawai aka samu ci gaba amma ta fannin tsaro da harkokin lafiya da ilimi da kuma bangaren cin hanci da rashawa a kasar nan har yanzu babu wani ci gaba da aka samu.
Dakta Abbati Bako ya kuma ce da shugabanin za su rinka bibiyar al’amuran kasar na kamar yadda sauran shugabannin kasa ke yi, to shakka babu za a samu ci gaba a wasu bangarorin.
Masanin siyasar ya shawarci mahukuntan kasar nan su kara baiwa bangarorin ilimi da tsaro da kuma lafiya fifiko domin ganin an farfado da tattalin arzikin.
You must be logged in to post a comment Login