Labarai
Ba mu da niyyar yin ƙarin kuɗin wutar lantarki- Minista

Gwamnatin Tarayya ta ce, ba ta da shirin yin ƙarin kuɗin wutar lantarki, duk da kalubalen da ke addabar fannin samar da wutar lantarki a kasar nan.
Ministan Makamashi, Joseph Tegbe ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai da ya gudana a babban birnin tarayya Abuja.
Ya ce gwamnati na kokarin magance basussukan fannin da suka kai kimanin tiriliyan N3.3.
Ministan ya ce a cikin kwanaki 100 na farko da ya fara aiki, an dawo da tashar wutar Alaoji mai ƙarfin megawatt 375.
Ya ce, gwamnati za ta mayar da hankali a watanni shida masu zuwa wajen ganin an samu ƙarin inganci da daidaito a samar da wutar lantarki.
You must be logged in to post a comment Login