Labarai
Kwamitin yakin zaɓen APC ya nemi Obi ya janye daga takara bisa zarginsa da barin Anambra da bashin dala Miliyan 92

Kwamitin yakin neman zaɓen jam’iyyar APC ya nemi Peter Obi, tsohon gwamnan Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC a 2027, da ya janye daga takarar saboda zargin barin jihar da bashin dala miliyan 92.
Mai magana da yawun kwamitin, Dele Alake, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a baya baya nan yana mayar da martani ga bayanan gwamnatin Anambra kan basussukan da aka ce gwamnatin Obi ta karɓa.
Gwamnatin jihar ta ce gwamnatin Obi ta karɓi bashin waje na dala miliyan 123, a cikin shekaru takwas da ya yi yana mulki, inda dala miliyan 92, kwatankwacin Naira biliyan 127, suka rage a matsayin basussuka har zuwa 30 ga Yuni 2026.
Ta ce an yi amfani da basussukan wajen ayyukan kiwon lafiya, ilimi, noma, kula da zaizayar ƙasa da sauran ayyukan ci gaba.
Sai dai Obi ya musanta hakan, yana cewa ya bar Anambra ba tare da bashin da ake binsa ba, tare da cewa bai bar bashin albashi, fansho, alawus ko kuɗin ’yan kwangila da aka kammala ayyukansu ba.
Alake ya ce bayanan gwamnatin Anambra sun saba wa ikirarin Obi, ya kuma zarge shi da rashin biyan wasu ma’aikatan gwamnati albashi a lokacin mulkinsa.
APC ta ce Obi ya taɓa yin alkawarin janyewa daga takarar shugaban ƙasa idan aka tabbatar da cewa ya bar Anambra da basussuka, inda ta bukaci ya cika wannan alkawari.
You must be logged in to post a comment Login