Labarai
Ba na goyon bayan ƙarin farashin mai – Kawu Sumaila
Tsohon mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan majalisar wakilai Abdurrahman Kawu Sumaila ya ce, baya goyon ƙarin farashin mai da gwamnatin tarayya ta yi.
Kawu Sumaila ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio, yana mai cewa, tsarin da gwamnatin tarayya ke bi a yanzu ya saɓa da tsarin da talakawan ƙasa suka zaɓe ta a kai.
“Talakawa sun zaɓi gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne domin su samu sauyi daga mulkin jam’iyyar PDP, amma sai ga shi har yanzu salon bai canza ba, kasancewar talakan ƙasa na ci gaba da fuskantar matsi da tsadar rayuwa” a cewar sa.
Kawu Sumailan ya ƙalubalanci ƴan kishin ƙasa da magoya bayan shugaba Buhari na haƙiƙa da kuma jam’iyyun adawa kan su fito su nuna rashin amincewar su da yin ƙarin farashin man.
Ku kasance da Freedom Radio da ƙarfe 6 na safiyar gobe Alhamis domin jin cikakken labarin a shirin mu na An Tashi Lafiya.
You must be logged in to post a comment Login