Labaran Kano
Ba sai an aikata laifi za mu ci abinci ba -Lauyoyi
Kungiyar lauyoyi ta kasa reshen jihar Kano, ta bayyyana cewa, maganganun da wasu mutane ke yadawa na cewa sai matsaloli sun faru an kai kara kotu sannan suke samun abinci, hakan ba gaskiya ba ne.
Shugaban kungiyar Barista Musa Abdullahi Lawan ne, ya bayyana hakan a tattaunawarsa da Freedom Radio.
Shugaban kungiyar ya ce, ba lallai ne sai wani ya aikata laifi ba sannan lauya zai samu abinda zai ci tare da iyalansa kamar yadda wasu ke yadawa.
Haka kuma ya kara da cewa, babu yadda za a yi ka raba mutane da aikata laifuka sai dai a samar da hanyoyin da za a bi a takaita yawan aikata laifuka.