Labarai
Ba wanda aka bawa filin tashar rijiyar zaki-Gwamnatin Kano
Gwamnatin jihar Kano ta musanta batun cewa ta rabawa wasu mutane filaye a tashar mota ta Rijiyar Zaki, inda ta bukaci jama’a da su yi watsi da batun domin ba shi da tushe balle makama.
Mai Magana da yawun gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar aka rabawa manema labarai.
Sanarwar ta bayyana cewa ‘wasu marasa kishin Kano ne ke kokarin shafawa gwamnatin jihar kashin kaji domin kawar da hankalin jama’a daga irin nasarorin da aka samu kawo yanzu’.
A cewar Sunusi ‘masu wararen ne suka bukaci gwamnati ta sauya musu fasalin gurin domin guraren su bunkasa kuma su kara daraja a cikin birnin Kano’.
Rahoton: Abdulkadir Haladu Kiyawa
You must be logged in to post a comment Login