Labarai
ba za mu lamunci amfani da kafofin yaɗa labarai don tayar da tarzoma a zaɓen 2023 ba – NBC
Hukumar kula da kafafen yaɗa labarai ta ƙasa NBC ta ce, ba za ta lamunci yin amfani da kafofin yaɗa labarai don tayar da tarzoma a zaɓen 2023 ba.
Shugaban hukumar Alhaji Balarabe Shehu Ilela ne ya bayyana hakan a wata ziyara da ya kai fadar gwamnatin Kano.
Ya ce, “A shirye muke don ganin yan siyasa ba su yi amfani da kafofin yaɗa labarai don cimma buƙatun su ba, ta hanyar tayar da tarzoma tsakanin al’umma”.
Alhaji Balarabe Ilela ya ce, haƙƙin masu kafafen yaɗa labarai ne na ganin sun hana yan siyasa yin amfani da kafafen don yin ɓatanci ga wasu.
“Dokokin hukumar mu sun hana bai wa kowa damar yin ɓatanci ga dan uwan su ko kuma yin kalaman da za su tayar da tarzoma”in ji Illela.
You must be logged in to post a comment Login