Labarai
Gwamnatin Zambia ta yi watsi da tallafin kudi da Amurka ke shirin bata

Gwamnatin kasar Zambia ta ce ba za ta amince da shirin taimakon kuɗaɗen tallafin lafiyar Amurka ba, wanda akai masa dabaibayi da wasu shariɗodin da suka kunshi ba su damar kai hannu a kan ma’adinan ƙasar ma su ɗimbin daraja.
Ministan harkokin wajen Zambia Mulambo Haimbe ne ya tabbatar da hakan da ya ce Amurkar ta musu tayin dala biliyan biyu a matsayin tallafin kula da harkokin lafiya nan da shekaru biyar ma su zuwa.
Ministan ya kuma ce wani babban abin damuwa shi ne yadda Amurka ta gindaya yarjejeniyar kaiwa ga ma’adinan Zambia a matsayin ɗaya daga cikin shariɗoɗin bada tallafin kuɗaɗen.
Rahotanni sun ce ƙasashen Afirka da dama sun rattaɓa hannu a kan irin wannan yarjejeniya da Amurka, sai dai ƙasashen Ghana da Zimbabwe sun yi watsi da ita.
You must be logged in to post a comment Login