Labaran Wasanni
Babban burina naga na lashe kyautar Ballon d’Or – Benzema
Dan wasa Real Madrid da kasar France Karim Benzema ya ce burinsa shine shiga sahun ‘yan wasan da suka taba lashe kyautar gwarzon dan wasan Duniya ta Ballon d’Or.
Benzema dai tuni ya shiga jerin ‘yan wasa 30 da za’a zaba domin lashe kyautar ta shekarar 2021.
Benzema mai shekaru 33 a kakar wasannin da ta gabata shine ya kasance dan wasa na biyu mafi zura kwallo a gasar La Liga.
Inda a yanzu kuma shine ke jagorantar yawan zura kwallaye a gasar ta kasar Sifaniya da kwallaye 9.
“Mafarkina shine ace na lashe kyautar Ballon d’Or, kuma ina saran lokacin hakan ne ya yi yanzu,” a cewar Benzema a zantawarsa da Canal+
“Naga yadda ”yan wasan da kusan nake koyi da su wato R9 [Ronaldo] ko kuma Zizou [Zidane] sukai wasa a Real Madrid kuma suka lshe Ballon d’Or,”
Sai dai tsohon mai horar da Real Madrid da kasar Faransa Zidane tuni ya amince dan wasa Benzema ne ka iya lashe kyautar a wannna lokacin.
Wannnan na zuwa ne bayan da mujallar wasanni ta kasar Faransa ta fitar da jerin ‘yan wasa 30 da kinsu daya zai lashe kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2021.
Hukumar ta sanar da hakanne a ranar Juma’a 08 ga Oktoban shekarar 2021.
Bikin bada kyautar dai zai gudana a birnin Paris na kasar Faransa a ranar 29 ga Nuwamba mai kamawa.
Cikin jerin ‘yan wasa 30 da za suyi takarar lashe kyautar ta shekarar
2021 ta Ballon d’Or sun hada da…………..
Cesar Azpilicuerta
Nicolo Barella
Karim Benzema
Leonardo Bonucci
Giorgio Chiellini
Kevin De Bruyne
Ruben Dias
Gianluigi Donnarumma
Bruno Fernandes
Phil Foden
Erling Haaland
Jorginho
Harry Kane
N’Golo Kante
Simon Kjaer
Robert Lewandowski
Romelu Lukaku
Riyad Mahrez
Lautaro Martinez
Kylian Mbappe
Lionel Messi
Luka Modric
Gerard Moreno
Mason Mount
Neymar
Pedri
Cristiano Ronaldo
Mohamed Salah
Raheem Sterling
Luis Suarez
Kopa Trophy shortlist:
Mason Greenwood
Bukayo Saka Pedri,
Jeremy Doku, Ryan Gravenberch,
Jamal Musiala, Florian Wirtz,
Jude Bellingham, Giovanni Reyna,
Nuno Mendes.
You must be logged in to post a comment Login