Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Babban burina naga na lashe kyautar Ballon d’Or – Benzema

Published

on

Dan wasa Real Madrid da kasar France Karim Benzema ya ce burinsa shine shiga sahun ‘yan wasan da suka taba lashe kyautar gwarzon dan wasan Duniya ta Ballon d’Or.

Benzema dai tuni ya shiga jerin ‘yan wasa 30 da za’a zaba domin lashe kyautar ta shekarar  2021.

Benzema mai shekaru 33 a kakar wasannin da ta gabata shine ya kasance dan wasa na biyu mafi zura kwallo a gasar La Liga.

Inda a yanzu kuma shine ke jagorantar yawan zura kwallaye a gasar ta kasar Sifaniya da kwallaye 9.

“Mafarkina shine ace na lashe kyautar Ballon d’Or, kuma ina saran lokacin hakan ne ya yi yanzu,” a cewar Benzema a zantawarsa da Canal+

“Naga yadda ”yan wasan da kusan nake koyi da su wato R9 [Ronaldo] ko kuma  Zizou [Zidane] sukai wasa a  Real Madrid kuma suka lshe  Ballon d’Or,”

Sai dai tsohon mai horar da  Real Madrid da kasar Faransa  Zidane tuni ya amince dan wasa Benzema ne ka iya lashe kyautar a wannna lokacin.

Wannnan na zuwa ne bayan da mujallar wasanni ta kasar Faransa ta fitar da jerin ‘yan wasa  30 da kinsu daya zai lashe kyautar Ballon d’Or ta shekarar  2021.

Hukumar ta sanar da hakanne a ranar Juma’a 08 ga Oktoban shekarar 2021.

Bikin bada kyautar dai zai gudana a birnin Paris na kasar Faransa a ranar 29 ga Nuwamba mai kamawa.

Cikin jerin ‘yan wasa 30 da za suyi takarar lashe kyautar ta shekarar

2021 ta Ballon d’Or sun hada da…………..

Cesar Azpilicuerta

Nicolo Barella

Karim Benzema

Leonardo Bonucci

Giorgio Chiellini

Kevin De Bruyne

Ruben Dias

Gianluigi Donnarumma

Bruno Fernandes

Phil Foden

Erling Haaland

Jorginho

Harry Kane

N’Golo Kante

Simon Kjaer

Robert Lewandowski

Romelu Lukaku

Riyad Mahrez

Lautaro Martinez

Kylian Mbappe

Lionel Messi

Luka Modric

Gerard Moreno

Mason Mount

Neymar

Pedri

Cristiano Ronaldo

Mohamed Salah

Raheem Sterling

Luis Suarez

Kopa Trophy shortlist:

Mason Greenwood

Bukayo Saka Pedri,

Jeremy Doku, Ryan Gravenberch,

Jamal Musiala, Florian Wirtz,

Jude Bellingham, Giovanni Reyna,

Nuno Mendes.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!