Kiwon Lafiya
Babban jojin kotun tarayya ya fitar da jadawalin hutun manyan kotunan kasar nan
Babban Jojin babbar kotun tarayya da ke Abuja mai Shari’a Abdul-Kafarati ya fitar da jadawalin yadda hutun Manyan Kotunan kasar nan zai kasance a bana.
Mai Shari’a Kafarati ya sanar da cewa manyan kotunan za su fara hutun ne daga ranar Litinin 9 ga watan Yuli zuwa Juma’a 14 ga watan Satumbar bana, sannan su dawo bakin aiki a ranar 17 ga watan na Satumba.
Alkalin ya bayyana cewa sanarwar ta yi daidai da sashe na 46 doka ta 4(d) cikin baka na kundin gudanar da Shari’a a manyan Kotuna na shekarar 2009.
Yayin hutun dai Kotun Abuja za ta kula Shari’o’in da suka shafi shiyyar Abuja, da Arewa maso tsakiya da Arewa maso yamma da kuma Arewa maso gabashin kasar nan.
Kotun Lagos kuma za ta kula da Shari’o’in da suka fito daga Yammacin kasar nan, yayin da ta garin Fatakwal za ta kula da shiyyar Kudu maso kudanci da kuma gabashin kasar nan.
Alkalan da za jagoranci zaman kotun Abuja su ne mai Shari’a Babatunde Quadri da Nnamdi Dimgba, sai mai Shari’a Chuka Obiozor da kuma Muslim Hassan.
A Fatakwal kuma akwai Alkalai irin su Hillary Oshomah da Adamu Muhammad.