Labarai
Gwamnatin Kano ta duba ingancin ayyuka 106 da ake gudanarwa kan fiye da Biliyan 48

Gwamnatin Jihar Kano ta ce, ta gudanar da aikin sanya ido da tabbatar da ingancin ayyukan raya ƙasa guda 106 da ake gudanarwa a ƙananan hukumomi shida na jihar, waɗanda jimillar kuɗin kwangilolinsu ya kai kusan naira biliyan 48.miliyan 910.
Kwamishinan Ma’aikatar bibiya da tabbatar da ingancin ayyukan da gwamnati ke gudanarwa Kwamared Nura Iro Ma’aji Sumaila, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai, na wata-wata kan ayyukan da hukumar ke yi wanda ya bayyana cewa, wannan aiki sun gudanar da shi ne a watan Satumban bana a ƙananan hukumomin Kabo da Dawakin Tofa da Tofa da Shanono da Gwarzo da kuma Bagwai.
Ya ce daga cikin ayyukan guda 106, an kammala ayyuka 80, wanda ya kai kusan kashi 75.5 cikin 100, yayin da ayyuka 20 ke matakai daban-daban na kammalawa, sannan an kuma bayar da ayyuka shida kwangila a baya-bayan nan, wadanda su ka haɗa da na hanyoyi da makarantu da cibiyoyin lafiya da gina ofisoshin rundunar tsaro ta Neighbourhood Watch da sanya fitiluna kan tituna masu amfani da hasken rana da gina magudanan ruwa da samar da ruwan sha.
Kwamishinan ya ƙara da cewa ma’aikatar na ƙarfafa amfani da fasahar zamani wajen sanya ido kan ayyukan gwamnati, ta hanyar ƙirƙiro wasu shafukan Internet guda biyu domin tabbatar da gaskiya, riƙon amana, bin ƙa’idojin kwangila da tabbatar da an samu ƙimar kuɗin da aka kashe.
Kwamared Nura Iro Ma’aji ya ce, ma’aikatar za ta ci gaba da sa ido kan ayyukan raya ƙasa a ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano, tare da bibiyar ayyukan da suka samu tsaiko ko waɗanda ba a kammala yadda ya kamata ba.
You must be logged in to post a comment Login