Siyasa
Babu banbanci tsakanin jam’iyyun APC da PDP –Bashir Jantile
A wata tattaunawa da tashar Freedom Radio ta yi da masanin harkokin siyasar duniya Bashir Hayatu Jantile, ya bayyana cewa duk manyan jam’iyyun kasar nan watau jam’iyyar APC mai mulki da kuma jam’iyyar adawa ta PDP duk tafiyarsu daya.
A cewarsa, “dukkan jam’iyyun da kuma shugabannin da mambobin su duk basa yin abubuwan da suka dace ta yadda ake kin hukunta wadanda ake zargi da aikiata almundahana da dukuiyar kasa.”
Ya ce a shekarar 2015, shugabana kasa Muhammadu Buhari, ya yi ikirarin hukunta wadanda ake zargi da barnatar da dukiyar kasa, saidai bai cika alkawarin ba.
Haka kuma ya ce, masu tunanin cewa shugaba Buhari zai daure Bola Tinunbu kawai suna bata wa kansu lokaci ne domin.
Ya kuma kara da cewa, “cikin dukkan jam’iyyun biyu babu wadda ta taba hukunta shugaba ko kuma mai rike da wani mukami da suka taba hukuntawa sakamakon aikata wani laifi.”
Masanin harkokin siyasar, ya kuma ce, “kamata ya yi, shugaban kasar ya dauki salon mulkin da ya yi nab a sani ba sabo lokacin da yake mulkin soja, da tuni ya gyara kasar nan.”