Labarai
Babu ranar komawa makaranta – Buhari
Gwammatin tarayya ta ce ba zata bude makarantun dake karkashin ta ba, saboda rubuta jarrabawar WAEC.
Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu ne ya sanar da hakan, ta cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce gwamnati ba za ta bude makarantu nan kusa ba, saboda jarrabawar WAEC, sai dai hukumar shirya jarrabawar ta yammacin Africa wato WAEC ta jinkirta rubuta jarrabawar.
Malam Adamu Adamu ya ce, yanzu ba lokaci ne da yakamata a bude makarantu ba, a don haka ya nemi gwamnatocin jihohi kan su mutunta matakin na gwamnatin tarayya.
You must be logged in to post a comment Login