Labaran Kano
Bai dace a dinga cefanar da wuraren wasanni ba a Kano- Masanin motsa jiki
Masani a bangaren koyar da ilimin wasanni da motsa jiki wato PHE a kwalejin Ilimi ta tarayya FCE Kano Dr. Isyaku Labaran Fagge, yace ba da-idai bane gwamnatin jihar Kano ta rika yanka filayen wasanni a na cefanar dasu ga ‘yan siyasa.
Dr, Isyaku Labaran Fagge ya bayyana hakan ne a yayin zantawar sa da wakilin gidan Radio Freedom Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa kan batun amfanin guraren wasanni a harkar koyo da koyarwa.
Masanin ya kara da cewa, yin hakan na haifar da rashin guraren wasanni na rage yawan aikata manyan laifuka a tsakanin matasa kuma hakan zai jawowa harkar Ilimi koma baya.
Dr. Isyaku Labaran Fagge ya kara da cewa kamata ya yi gwamnatoci su rika samar da ingantattun guraren wasanni iri daban-daban bawai a rika cefanar dasu ba, kasancewar yawan motsa jiki na matukar taimakawa wajen inganta lafiya kamar yadda likitoci ke fada.
Rundunar Sojan sama na Atisaye a Kano
civil Defense: zata fitar da jadawali na auna yanayin ayyukan kwakwalwarsu
Kazalika masanin na cewa matukar za’abar matasa suna zama babu guraren wasanni to babu shakka matasan zasu shiga tunanin aikata laifuka harma da yawan shaye – shayen miyagun kwayoyi.
A don haka akwai bukatar samar da guraren wasanni a kowacce unguwa a jihar Kano , kuma gine irin wadannan guraren wasa ba alkairi bane a nan Kano, saboda koda an gine guraren wasannin ba’a samar da wasu sabbi, A cewar sa.