Labarai
Bankin CBN ya ce akwai bukatar samar da manufofin bunkasa tattalin arzikin kasa
Babban bankin kasa, CBN ya ce akwai bukatar samar da kwararan manufofin da za su lura da bunkasar tattalin arziki da kudaden da ake samu ta yadda za’a samu ci gaba mai dorewar bayan fita daga masassarar tattalin arziki da kasar nan ta yi.
Gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele ne ya bayyana haka jiya a wajen bude taron karawa juna ilimi a Abuja mai taken ‘samar da tattalin arziki mai dorewar bayan fita daga matsin tattalin arziki’.
Emefiele ya ce samar da tattalin arziki mai dorewa na bukatar kyawawan manufofi tsakanin jiga-jigan bangarorin da ke tsara manufofin tattalin arzikin a kasa.
Ya kara da cewa irin wadannan bangarori sun hada da tattalin arziki da shiga-da-fitar kudi da kuma musayar kudade da zai mayar da hankali kan bunkasa harkokin noma da tallafawa kananan masana’antu.
Gwamnan babban bankin ya ce, samar da wadannan manufofi zai taimakawa kasar nan wajen baza komarta zuwa karin wasu bangarorin tattalin arzikin da ba na mai kawai ba.