Labarai
Bankin duniya zai baiwa Kano da wasu jihohi bashin kudi
Bankin Duniya zai bai wa jihar Kano da wasu jihohin kasar nan guda shida bashin kudi da ya kai dala miliyan dari biyar domin bunkasa harkokin karatun ‘ya’ya mata.
A cewar bankin na Duniya rancen wanda babu kudin ruwa a cikinsa, za ayi amfani da shine wajen bunkasa karatun mata a matakan sakandire a jihohin guda bakwai.
Hakan na cikin wata sanarwar ce da bankin na Duniya ya fitar yau a Abuja wanda ke cewa, kudin wani bangare ne na ,kudaden da bankin ke bai wa kasashe masu tasowa don gudanar da ayyukan raya kasa.
Jihohin da za su amfana da bashin na bankin Duniya don bunkasa karatun ilimi mata sun hada da: Kano da Kebbi da Kaduna da Katsina da Borno da Plateau da kuma Ekiti
Haka zalika sanarwar ta kara da cewa, kudaden za su kuma taimaka wajen koyar da sana’oin dogaro da kai ga mata da kuma wayar da kan mata kan harkokin kiwon lafiya da sauransu.
You must be logged in to post a comment Login