Kowane Gauta
Bashir Sanata ya soki Buhari kan mawuyacin halin da ‘yan Najeriya ke ciki
Bashir Sanata ya soki gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan mawuyacin halin da ‘yan Najeriya ke ciki a halin yanzu.
Bashir Sanata a jam’iyyar PDP na kungiyar kwankwaso kawai kalubalantar gwamnatin tarayya yayi kan irin matsalolin da ‘yan kasa suke a cikin ta.
Bashir Sanata ya bayyana haka ne ta cikin shirin Kowane Gauta na Freedom radio, yana mai cewa gwamnatin Buhari ta yi alkaura da dama amma sun gaza tabuka komai ga talakawan Najeria.
Bashir Sanata yace talakawan Najeria sun yi tsammanin samun sauki a gwamnatin Shugaba Buhari , amma yanzu haka duk talalawan kasar sun cire tsammani a gwamnatin baki daya.
You must be logged in to post a comment Login