Manyan Labarai
Bayan da aka yi karin farashin fetur da wuta kayan gwari bai sauya ba – kungiya
A ya yin da ake cigaba da fuskantar tashin farashin kayan abinci a nan Kano masu sana’ar sayarda kayan miya da akafi sani da kayan gwari sunce sakamakon albarka da Allah yayiwa wannan damuna kayan gwari bai kara farashi ba a yanzu.
A cewar shugaban kungiyar masu sayarda kayan gwari a kasuwar Sharada Alhaji Na’iya a wata zantawa da wakilin Freedom Radio Abdulkarim Muhammad Tukuntawa yayi dashi yace an samu matsalar tsadar kaya a lokacin zaman gida na kulle amma banda yanzu.
Alhaji Na’iya ya kara da cewa farashin kayan miya musamman buhu ko Kwando a yanzu ya ragu sosai ba kamar yadda aka saba siyarwa ba a baya, sai dai yace kananan ‘yan kasuwa masu sayarwa kadan ne a yanzu suke samu da tsada.
Sallah : Yadda kayan miya da man gyada suka yi tashin gwauron zabi a Kano
Nazari kan kalubalen da masu Lambu ke fuskanta a Kano
Na’iya yace a yanzu magidanta zasu rika samun kayan miya cikin farashi mai saukin gaske musamman a wannan lokaci na damuna sakamakon kayan miya ya fara samuwa sosai a gari wanda dama karancin suna ne ke jawo tsadarsu.
You must be logged in to post a comment Login