Kiwon Lafiya
Bayar da gudunmowar jini kyauta zai taimaka wajen rage mace-mace – NBTS
Bayar da gudunmowar jini na taimakawa wajen rage mace-macen marasa lafiya dake bukatar jini a asibitoci.
Babban jami’in cibiyar bayar da jini ta kasa Dakta Joseph Amedu ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da jawabi a taron bikin ranar bada gudunmowar jini ta duniya.
Amedu ya ce, “Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce Najeriya na bukatar a kalla ma’aunin Units miliyan 2 na jini a kowace shekara amma Units dubu dari 5 ake samu a kowace shekara.”
“Ya kamata matasa su rinka bayar da gudunmowar jini kyauta domin ceton rayukan al’ummar Najeriya, “ inji Amedu.
Taron da jaridar Punch ta hada kuma aka gudanar ta kafar Internet na dauke da taken: Me yasa Najeriya ke bukatar karin masu ba da gudunmowar jini kyauta.
You must be logged in to post a comment Login