Labarai
Bill Gates ya nemi Najeriya ta ci gaba da rigakafin Polio
Fitaccen attajirin nan kuma shugaban gidauniyar Bill and Melinda Gates, Mr Bill Gates, ya ce, duk da cewa hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce babu cutar polio a kasar nan a wannan lokaci, amma yana da kyau hukumomi su ci gaba da gudanar da allurar rigakafi ga kananan yara.
Ya ce, abin alfahari ne kuma labari mai dadin ji yadda aka kawo karshen cutar, sai dai ba daidai bane a ce kuma za ayi watsi da digon rigakafin cutar domin kawar da duk wani burbushin cutar a kasar nan.
Mista Bill GATES ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke wata ganawa da gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da attajirin nan Alhaji Aliko Dangote ta kafar internet.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai na gidan gwamnatin jihar Kano Aminu Yassar, ta ce, shima ministan lafiya Dr Osagie Ehanire yana cikin mahalarta taron.
Sanarwar ta kuma ruwaito shugaban gidauniyar Dangote Alhaji Aliko Dangote na yabawa gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje sakamakon jajircewarsa wajen ganin bayan cutar.
You must be logged in to post a comment Login