Labarai
Buhari na jagorantar taron majalisar zartarwa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana jagorantar taron majalisar zartaswa ta kasa a Abuja.
Rahotanni sun ce kafin fara taron sai da aka gudanar da shiru na ‘yan mintuna don karrama mahaifin gwamnan jihar kwara kuma lauya na farko a arewacin kasar nan Alhaji Abdulganiyu Abdurrazak wanda ya rasu a baya-bayan nan a birnin tarayya Abuja.
A makon jiya ne dai mahaifin na gwamnan jihar Kwara ya rasu bayan fama da wata gajeruwar rashin lafiya.
You must be logged in to post a comment Login