Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari na wata ganawar sirri da shugaban ƙasar Turkiyya

Published

on

Shugaban ƙasa Muhammdu Buhari na wata ganawar sirri da shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a Villa da ke Abuja.

Tun da fari dai Recep Tayyip Erdogan ya isa Abuja da yammacin ranar Talata don yin wata tattaunawa ta musamman da shugaba Buhari.

Ana dai sa ran shugabannin biyu za su tattauna kan abubuwa 24 da suka ƙulla yarjejeniyar fahimtar juna a kai.

Ziyarar ta shugaba Recep Tayyip Erdogan na cikin wata sanarwar da mataimaki na musamman ga shugaba Buhari kan harkokin yaɗa labarai Mallam Garba Shehu ya fitar.

Sanarwar ta ce, ana sa ran Recep Tayyip Erdogan zai ƙaddamar da cibiyar kula da al’adu ta ƙasar Turkiyya a Abuja.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!