Labarai
Buhari ya jinjina wa matasan Kano kan ƙin shiga zanga-zangar EndSars

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yaba wa matasan jihar Kano bisa jajircewarsu wajen tabbatar da zaman lafiya a lokacin zanga-zangar EndSars.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne ta bakin mai taimaka masa kan rayuwar matasa Barista Isma’il Ahmad.
A yayin taron jin ra’ayin matasan Kano da aka gabatar ranar Lahadi a ɗakin taro na gidan Mumbayya.
Barista Isma’il Ahmad ya yi yi alƙawarin cewa za su haɗa kai da sauran ƴan Kano masu riƙe da muƙamai a gwamnatin tarayya wajen inganta rayuwar matasa.
Labarai masu alaka:
Yadda Buhari ya karbi bakuncin Sarkin Kano a fadar sa
Dattijan Kano sun nemi Buhari ya ki amincewa da bukatar Ganduje
You must be logged in to post a comment Login