Labarai
Buhari ya nemi hukumomin da su tabbatar sun karfafa dokar yaki da Covid-19

Gwamnatin Tarayya ta umarci dukkanin hukumomin da su tabbatar sun karfafa dokar yaki da annobar Covid-19 mai saurin yadua, yayin da ake fargabar barkewarta a karo na biyu.
Shugaban kwamitin fadar shugaban kasa kan yaki da kwayar cutar, Boss Mustapha, shine ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja.
Boss Mustapha wanda shine sakataren gwamnatrin tarayya, ya ja hankalin ‘yan Najeriya game da tsauraran matakan da za a dauka kan duk wanda aka samu da laifin karya dokar yaki da cutar Korona.
You must be logged in to post a comment Login